✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta soke takarar Sanata Adamu Aleiro

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Birnin-Kebbi, ta dakatar tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Muhammadu Adamu Aliero daga takarar dan Majalisar Dattijawa na mazabar…

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Birnin-Kebbi, ta dakatar tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Muhammadu Adamu Aliero daga takarar dan Majalisar Dattijawa na mazabar Kebbi ta Tsakiya a jam’iyyar PDP.

BBC ya ruwaito Kotun ta kuma bayyana Alhaji Haruna Sa’idu Dan D.O a matsayin halattaccen dan takarar sanata na PDP a zaben na shekara mai zuwa.

A watan Yunin wannan shekarar ne Sanata Aliero ya sauya sheka zuwa PDP daga jam’iyyar APC mai mulki, yana ikirarin lashe zaben fidda gwani na mazabar da aka sake yi.

Sai dai, Alhaji Haruna Saidu da ke neman takarar ya yi fatali da wannan ikirari, inda ya kalubalanci lamarin a gaban kotu.

Hakan na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da kotun ta hana Sanata Yahaya Abdullahi Argungu kasancewa dan takarar jam’iyyar PDP a mazabar Kebbi ta arewa.

Shi ma dai ya sauya sheka ne bayan kammala zaben fitar da gwani.