✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta soke zaben dan takarar gwamnan APC a Akwa Ibom

Kotun ta bayar da umarnin sake gudanar da sabon zabe nan da mako biyu masu zuwa.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Uyo, ta soke zaben fid-da-gwani na jam’iyyar APC wanda ya ayyana Mista Akanimo Udofia a matsayin dan takarar Gwamnan Akwa Ibom na Zaben 2023. 

Alkalin kotun, Mai shari’a Agatha Okeke, a hukuncin da ta yanke, ta bayar da umarnin sake gudanar da sabon zaben fid-da-gwani nan da mako biyu masu zuwa.

Okeke ta bayyana cewa, Kwamitin Zaben gwamnan APC, ya saba wa tanadin Dokar Zabe wajen gudanar da zaben fid-da-gwani, inda ta ce babu wata shaida da ke nuna cewa tsarin da aka yi na zaben ya yi daidai da dokar.

Okeke ta yi watsi da zargin da aka yi wa Udofia, ta kuma umarci jam’iyyar da ta sake gudanar da wani zaben, inda dan takarar gwamna zai fito.

Ta ce hujjojin da ke gaban kotu sun nuna cewa ba a gudanar da zaben ba a bisa tsari na doka ba, kuma zaben Udofia ya zama shi da babu duk daya ne.

Alkalin kotun ta bayar da umarnin cewa APC a cikin kwanaki 14, ta gudanar da sabon zabe sannan kuma ta bayar da umarnin hana wanda ake kara (Udofia) shiga sabon zaben fidda gwani.

Tun a ranar 26 ga watan Mayu, daya daga cikin manema takarar, Sanata Ita Enang, ya kalubalanci sahihancin sakamakon zaben a gaban kotu.

Kamfanin Dillancin labarai NAN), ya ruwaito cewa wadanda suka shigar da karar sun hada da Udofia, daga jam’iyyar APC da kuma Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), a matsayin wadanda ake kara na daya da na biyu da na uku.