✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haramta wa PDP shiga takarar gwamnan Zamfara daidai ne —Kotu

Wadanda suka gabatar da karar za su biya tarar naira dubu 100.

Wata Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Jihar Sakkwato, ta tabbatar da hukuncin hana dan takarar Gwamnan PDP a Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare shiga zaben 2023.

Wannan na zuwa ne bayan da kotun ta yi fatali da karar da jam’iyyar da kuma dan takarar suka shiga suna masu neman halascin shiga zaben na badi.

Kwamishinan Yada Labarai Jihar Zamfara, Ibrahim Magaji Dosara ne ya bayyana hukunci kotun cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

A cewar sanarwar, “daukaka karar ya saba wa hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau ta yanke a ranar 16 ga watan Nuwamba 2022, wanda ya soke zaben fid-da-gwanin dan takarar gwamna na jam’iyyar saboda rashin bin ka’idar Dokar Zabe ta 2022 da ka’idojin PDP.

“A cikin hukuncin wanda alkalai uku na Kotun Daukaka Kara suka yanke, Mai Shari’a M L Shuaibu JCA, Shugaban Kotun Daukaka Kara ta Sakkwato, wanda ya zartar da hukuncin, ya ce daukaka karar aiki ne na ilimi.

Sanarwar ta kara da cewa, “Saboda haka, an yi watsi da karar sannan wadanda suka gabatar da karar za su biya tarar naira dubu 100.”