✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare ‘barayin kananan yara’ a gidan yari

Ana zargin sun saci yara masu shekaru biyar da hudu ne ranar 25 ga watan Fabrairu

Kotu ta ba da umarnin tsare wasu mutum biyu a gidan yari saboda zargin satar kananan yara.

Kotun Majistare da ke Abakaliki ta tsare mutanen ne bayan an gurfanar da su ranar Talata kan zargin satar yara biyu masu shekaru biyar da kuma hudu.

Ya ce mutanen sun saci yaran ne ranar 25 ga watan Fabrairu a Agubai, Karamar Hukumar Ikwo da ke Jihar Ebonyi, kamar yadda dan sanda mai shigar da kara, Micheal Eze ya shaida wa kotun.

Bayan sun sun musanta zargin, Michael ya ki amincewa da buktar bayar da belinsu da cewa, “Muna tsoron za su iya saba sharuddan beli ga shi dama satar yaran ta riga ta haifar da damuwa ga dangin.’’

Don haka alkalin kotun, Nnenna Onuoha ta ba da umarnin tsare su tare da a mika batun zuwa Kotun Iyali inda za a ci gaba da shari’ar.

“Wannan shari’ar ce da ta shafi yara. Yanzu a kai shi zuwa Kotun Iyali, inda za a yi la’akari da neman belinsu,’’ inji ta.

Alkalin kotun ta kuma dage sauraron karar zuwa ranar 11 ga watan Maris don ci gaba da shari’a a Kotun Iyalin.