✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta tsare dan acaban da ya yi wa tsohuwa fyade a gidan yari

Alkalin kotun ya ki amsar rokon matashin, ya umarci a ci gba da tsare shi a gidan gyaran hali.

Kotu ta tsare wani matashi a gidan yari bisa zargin yi wa wata tsohuwa mai shekara 50 fyade.

’Yan sanda sun shaida wa kotun cewa matashin ya yi wa tsohuwar fyade ne lokacin da take kan hanyar zuwa gona.

Dan sanda mai shigar da kara, Isfekta Oriyomi Akinwale, ya shaida wa kotun cewa matashin ya aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Janairun 2021, a Karamar Hukumar Ikole-Ekiti da ke Jihar ta Ekiti.

Alkalin kotun, Cif Adefumike Anoma, ya ki saurarar rokon wnada ake karar, inda ya ba da umarnin ci gaba da tsare shi da a gidan yari.

Ya kuma ba da umarnin a mayar da kundin laifin nasa gaban Daraktan Gurfanar da masu Laifuka.

Alkalin ya dage zaman kotun zuwa ranar 4 ga watan Maris, 2021.