✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare matar da ta ba da daki ana lalata a Zariya

Ta ba wa magidanci hayar daki yana lalata da karamar yarinya.

Kotu ta tsare wata mai ’ya’ya biyu bisa zargin bayar da hayar daki a gidanta ana yin lalata.

An gurfanar da matar ce a Kotun Magistare da ke Kofar Fada a cikin birnin Zariya bisa zargin hada baki da yin lalata da mata da kuma yin garkuwa da yarinya.

Ana tuhumar da ne tare da wani mai mutum bisa aikata laifin da ya saba wa sashi na 59 da 230 da 368 na dokokin Final Kod.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Abdullahi Sarki ya shaida wa kotun cewa ’yan sanda sun kammala bincike a kan batun don haka a shirye suke domin ci gaba da shari’ar.

Mai shari’a, Zainab Garba ta ba da umarnin a mai da wadanda ake zargin zuwa Sashin Binciken Manyan Laifuffuka na Rundunar ’Yan sandan Jihar da ke Kaduna domin gudanar da sabon bincike.

A cewar Mai shari’a Zainab Garba, ta kasa fahimtar inda za a gurfanar da karamar yarinya da laifin cewa ta yi lalata yayin da take da aure, don haka sai ta soke belin da tunda farko ta ba wa wadanda ake zargin.

Wakilinmu ya ce bayanin da ’yan sanda suka gatabar wa kotu ya nuna cewa ranar 10 ga Agusta da misalin karfe 1:00 na rana mahaifin yarinyar ya kai karar wadanda ake zargin a ofishin ’yan sanda.

Ya bayyana musu cewa wani mutum ya dauki ’yarsa mai shekara 15 da aka sakaya sunanta zuwa gidan matar da ke Gwargwaje a Zariya.

Ya ce matar ta ba wa mutumin hayar daki a kan Naira dubu daya inda yake lalata da yarinyar wanda hakan ya yi sanadiyar da ta samu juna biyu.

A cewar takardar bayanan ’yan sandan, wanda ake zargin ya hada baki da tsohuwar matarsa suka dauke yarinyar suka tafi da ita Kano bayan kwana daya suka dawo da ita.

Daga bisani kuma suka tafi da ita garin Birnin Yero a Karamar Hukumar Igabi da ke Jihar Kaduna inda a can ma ta kwana biyu.