✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare shi saboda satar katin ATM din makocinsa

Wanda ake zargin ya cire kudi N200,000 bayan sace ATM din makocin nasa.

Wata kotun majistare a Jihar Kaduna ta daure wani matashi mai shekara 32, saboda satar katin ATM din makocinsa tare da cire kudi N200,000.

Ana dai tuhumar matashin da ke zaune a Ungwan Pama a Kaduna, da laifin aikata sata.

Dan sanda mai shigar da kara, Chidi Leo, ya shaida wa kotun cewar wanda ake zargin ya saci ATM din makocins nasa ne sannan ya cire kudi har N200,000 ba tare da saninsa ba.

Leo ya ce, bayan mutumin ya samu sakon fitar kudi, nan take ya garzaya zuwa banki don toshe katin cirar kudin.

Ya kara da cewar, an samu katin cirar kudin a wajen wanda ake zargin yayin da yake kokarin ciro kudi daga jakar ajiye kudin da ke aljihunsa.

Ya ce tuni aka mika lamarin ga  jami’an ’yan sanda don fadad bincike.

A cewarsa, laifin ya saba da tanade-tanaden sashe na 217 na kundin laifukan Jihar Kaduna na shekarar 2017.

Sai dai wanda ake zargin ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa a gaban kotun.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Emmanuel ya ba da belin wanda ake zargin kan kudi N150,000 tare da gabatar da mutum daya da zai tsaya masa.

Alkalin, ya ce dole ne wanda zai tsaya masa din ya kasance cikakken ma’aikacin gwamnatin Jihar Kaduna, sannan ya kasance wanda yake da shaidar biyan haraji na tsawon shekara biyu.

Daga nan sai ya dage zaman kotun har zuwa ranar 21 ga watan Fabrairun 2022.