✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare tsohon Akanta-Janar a gidan yari

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta tura tsohon Akanta-Janar na Tarayya Ahmed Idris zuwa gidan yari kan badakalar Naira biliyan 109.4.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ba da umarnin tsare dakataccen Akanta-Janar na Tarayya Ahmed Idris a gidan yari kan badakalar Naira biliyan 109.5.

Kotun ta ba da umarnin tisa keyar Ahmed Idris zuwa gidan yari ne bisa zarin sa da karkatar da kudaden gwamnati da sata da cin amana sata da ta’ammali da haramtattun kudade da kuma aikata manyan laifuka, ciki har da karbar rashawa ta Naira biliyan 15 a lokaci guda.

A safiyar Juma’a kotun ta bayar da umarnin bayan Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziki (EFCC) ta gurfanar da shi a karo na biyu.

An gurfanar da shi ne tare da hadiminsa, Godfrey Olusegun Akindele da Mohammed Kudu Usman da kuma kamfanin Gezawa Commodity Market and Exchange Limited.

Wadan ake zargin dai sun ki amsa tuhumar da ake musu, lamarin da ya sa kotu ta ce a tsare su har zuwa ranar 27 ga watan Yuli da muke ciki.

A ranar ce kuma za a saurari bukatar bayar da shi beli.

EFCC na zargin tsohon Akanta-Janar din na Tarayya ne kan aikata laifuka 14 tare da tsohon hadiminsa kan karkatar da Naira biliyan 84.4 da kumakarbar rashawar Naira biliyan biliyan 15 ta hannun wani hadiminsa, Geoffrey Olusegun Akindele.

A ranar 16 ga watan Mayu EFCC ta fara gurfanar da shi kan zargin amfani da matsayinsa wajen karbar Naira biliyan 84 da sunan kamfanin hadimin nasa Olosegun Akindele & Co.

Ana kuma zarginsa da karbar Naira biliyan 15 da aka canza su zuwa Dala a matsayin cin hanci domin ya yi amfani da matsayinsa ya sa a gaggauta biyan jihohi tara masu arzikin man kasho 13 cikin 100 da ake warew musu daga Asusun Gwamnatin Tarayya.