✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare wanda ya yi wa yarinya mai shekara 10 fyade

Wata kotu ta tsare mutumin da ake zargi da lalata karamar yarinya a gidan yari.

Kotun Majistare da ke zamanta a garin Ado-Ekiti ta daure wani mutum mai shekaru 40 a gidan yari bisa zargin sa da yi wa karamar yarinya fyade.

Mai shigar da kara gaban kotun, Caleb Leramo, ya ce wanda ake zargin ya yi wa yarinyar mai shekar 10 a duniya fyaden ne a ranar 23 ga watan Fabrairun 2021, a garin Ado-Ekiti.

Leramo, ya ce wanda ake zargin ya yi wa yarinyar wayo, ya ja ta zuwa dakinsa, inda ya lalata ta.

Bayan aikata laifin kuma, ya gargadi yarinyar da kada ta sanar da kowa abin da ya faru.

Leramo, ya ce laifin ya saba da sashe na 31 da kundin kare Kananan Yara na Jihar Ekiti, na shekarar 2012.

Mai shigar da karar ya roki, kotu ta tsare shi a gidan yari, har zuwa lokacin da Daraktan Lauyoyin Masu Gabatar da Kara (DPP) ya bayar da shawara ta fuskar shari’a.

Mai shari’a Misis Mojisola Salau, ta sauraron shari’ar zuwa ranar 14 ga Afrilun 2021.