✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tura Alhassan Doguwa gidan yari

Rundunar ’yan sandan Kano na zargin Alhassan Doguwa da kisan kai.

Wata Kotun Majistare da ke zamanta a Unguwar Nomansland ta Jihar Kano, ta tura Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa gidan wakafi.

Doguwa mai wakiltar kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada ya gurfana gaban kuliyar ce bisa zargin wasu laifuka masu alaka da hadin baki wajen aikata kisan kai, da raunata mutane da dama.

Haka kuma, ana zargin Doguwa da hannu a kunna wuta a ofishin jam’iyyar hamayya ta NNPP, wadda ta yi sanadiyyar kona wasu mutane da ke cikin ofishin.

A yayin zaman kotun na wannan Larabar, wanda ake zargin ya musanta tuhume-tuhumen da suka saba wa sassa na 114 da 221 da 247 na kundin penal kot.

Sai dai kuma Alkalin Kotun, Mai Shari’a Ibrahim Mansur Yola wanda ya bayar da umarnin ajiye wanda ake zargin a gidan gyaran hali, ya kuma dage sauraron karar zuwa ranar 7 ga watan Maris.

A wata sanarwa da rundunar ’yan sandan jihar ta fitar ranar Talata, ta ce Kwamishinan ’yan sandan jihar da ke lura da al’amuran zaben 2023 CP Muhammad Yakubu ne ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan zarge-zargen.

Sanarwar ta ce ana zargin dan majalisar na da hannu a kisan wasu mutum uku tare da raunata wasu mutum takwas a Karamar Hukumar Doguwa ranar 26 ga watan Fabrairu a lokacin da ake karba tare da tattara sakamakon zaben dan majalisar.

An dai yi ta yada hotuna da bidiyon wasu mutane da ake zargi an harba da bindiga a shafukan sada zumunta.

Tun daga nan kuma rundunar ’yan sandan ta gayyaci dan majalisar domin gudanar da bincike kan batun.

Sanarwar ta ce bayan da dan majalisar ya ki amsa gayyatar ne, rundunar ’yan sandan jihar ta kama shi a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke jihar.