✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar budurwa: Kotu ta tura wanda ake zargi gidan yari

Babbar Kotun Majistare da ke garin Kafanchan a Jihar Kaduna ta tura wani matashi dan shekara zuwa gidan gyara halinka saboda zargin satar yarinya ‘yar…

Babbar Kotun Majistare da ke garin Kafanchan a Jihar Kaduna ta tura wani matashi dan shekara zuwa gidan gyara halinka saboda zargin satar yarinya ‘yar kimanin shekara 15.

Alkalin kotun Abdul’aziz Ibrahim ya ki sauraron rokon wanda ake zargin saboda gaza kawo kwararan dalilai, inda ya yi umarnin da a sakaye shi har zuwa ranar 8 ga watan Yuli da ke tafe.

Mathias Joseph, mai shigar da kara daga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kaduna ya bayyana wa kotun tun da farko cewa an kawo rahoton ne ga Cibiyar Salama da ke sauraron koke-koken cin zarafin mata da kananan yara da ke garin Kafanchan inda daga nan aka tura batun zuwa ga jami’an tsaron Sibil Difens (NCDC) don ci gaba da bincike.

Joseph ya ce wanda ya kawo karar daga garin Jagindi Tasha yake a Karamar Hukumar Jama’a, inda ya yi zargin cewa wanda ake hutuma ya aiko da bukatar neman auren budurwar, amma suka ki amincewa da hakan, sannan shi da Mai Unguwarsu suka ja masa kunne da ya fita harkar ‘yarsu saboda rashin aminta da dabi’unsa.

Joseph ya ce wanda ake zargi ya bayyana daga baya cewa shi ya dauki yarinyar zuwa wata maboya.