✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta umarci a kyale Nnamdi Kanu ya kalli wasannin Liverpool

Kotun ta ce dole a kyale shi ya kalli dukkan wasannin kungiyar

Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Mai Shari’a Binta Murtala Nyako, ta umarci Hukumar Tsaro ta DSS da ta kyale Nnamdi Kanu, ya kalli wasannin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool daga inda yake tsare.

Kanu dai shi ne Shugaban haramtacciyar kungiyar nan ta masu fafutukar kafa kasar Biyafara ta IPOB.

Ba da umarnin ya biyo bayan bukatar da lauyansa, Mike Ozekhome, SAN ya shigar a gaban kotun, inda ya ce duk lokacin da ya ziyarci Kanun a inda yake tsare ba a ba shi damar ganin shi.

Sai dai Alkalin ta ce duk da umarnin da ta ba Kanun na canza riga, ya ci gaba da zuwa da wata riga kala daya mai ruwan madara a kowace ranar zaman kotun, ko da yake yana sa wasu a wasu wuraren.

Daga nan ne sai Mai Shari’a Binta Nyako cikin raha ta ce ita mai goyon bayan Liverpool ce, sannan ta tambayi lauya Ozekhome, inda shi ma ya amsa mata da eh.

Sai ta tambayi Nnamdi Kanu ko kungiyar Chelsea yake goyon baya duba da irin kayan da yake sakawa.

Daga nan ne sai ya mike tsaye ya ce, “Tun ina dan shekara bakwai ni dan Liverpool ne.”

Jin hakan ne ya sa Alkalin ta umarci Daraktan Shari’a na hukumar DSS, wanda yake a cikin kotun a lokacin da ya kyale Kanu ya rika kallon wasannin kungiyar da yake goyon baya.

Ta ce “Dole ku kyale wanda ake kara ya kalli dukkan wasannin da suke bugawa,” inda ta ce za ta bayar da umarni a kan haka.

Sai dai Daraktan na DSS ya ce ofishin nasa a kodayaushe yana ba Nnamdi Kanu damar kallo a akwatin talabijin. (NAN)