✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta umarci Gwamnatin Najeriya ta bai wa mata kashi 35 na mukamai

Ba a yi adalci ba ga mata wadanda suka kai miliyan 70 na yawan ‘yan Najeriya.

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da manufar daidaiton jinsi ta hanyar bai wa mata ikon rike kashi 35 cikin 100 na mukaman gwamnati.

Da yake yanke hukunci kan karar da wani rukunin mata ya shigar, Mai Shari’a Okorowo Donatus ya amince da korafin masu karar wadanda suka ce ana nuna wa mata wariya a wajen nadin manyan mukamai na gwamnati.

Mai shari’ar ya yi watsi da hujjojin da lauyan gwamnatin ya gabatar na cewa masu karar sun gaza gabatar da hujjar da za ta nuna cewa ana nuna musu wariya.

Sai dai mai shari’ar ya kafa hujja da sashe na 42 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya domin kare matsayar masu karar, inda ya ce cikin ministoci 44 da ake da su shida ne kawai mata, wanda wannan wariya ce a zahiri, kuma abin ya fi muni a ma’aikatun gwamnatin.

Ya kara da cewa ba a yi adalci ba ga mata wadanda suka kai miliyan 70 na yawan ‘yan Najeriya.

BBC ya ruwaito cewa an yi ta ihu da murna da wake-wake a Babbar Kotun Tarayya bayan yanke wannan hukunci da ya yi wa matan Najeriya dadi.