✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta umarci mata ta rika karbe kudin gidan hayar mijinta a Kaduna

Kotun ta ba wa matar damar sanya ’yan haya a gidan mijin.

Kotun Musulunci da ke zamanta a Rigasa a Jihar Kaduna ta umarci wata matar aure ta bayar da gidan mijinta haya ta rika kabar kudin domin ciyar da ’ya’yansu da biyan kudin makarantarsu.

Alkalin kotun, Malam Abubakar Salisu-Tureta ne, ya yanke hukuncin cewa matar ce za ta karbi kudin hayar tare da ajiyewa a wajenta, domin ta rika sarrafa kudin yadda ya kamata domin kula da ’ya’yansu.

Matar ta shaida wa kotun cewa, “A yanzu duka yaran suna gida a zaune. Ba sa zuwa makaranta; A gaskiya ma har sai da aka ci zarafin daya ta hanyar lalata saboda an yaudare shi da abinci.’’

Alkalin, ya yanke hukuncin ne a ranar Talatar, bayan da matar ta roki kotun ta sa mijin nata, ya rika ciyar da su da kuma daukar dawainiyarsu.

Tun asali matar ta shaida wa kotun cewa ita ce take ciyar da kanta da kuma ’ya’yansu takwas ta hanyar dan kasuwancin da take yi a cikin gida, amma kuma kudin da take samu ba zai isa daukar nauyin karatun yaran ba.

Da yake yi wa kotun jawabi, mijnin nata ya ce ya kasa kula da ’ya’yan nasu takwas ne saboda rashin aikin yi.

Amma ya ce idan ya yi buga-buga ya samu kudi yana kawo abin da ba a rasa ba wanda za su sanya a bakin salatinsu.

Alkalin kotun ya dage shari’ar har zuwa ranar 8 ga watan Maris 2022, don yanke hukunci.