✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta umarci Sarkin Dubai ya biya tsohuwar matarsa Dala miliyan 500

A lokacin da take Dubai ana ba Gimbiya Haya Fam miliyan 91 a shekara domin kula da gida da kuma kyaututtuka.

Kotu ta umarci Sarkin Dubai, Sheikh Mohammed bin Rashid al-Maktoum, ya biya tsohuwar matarsa, Gimbiya Haya, kimanin Dala miliyan 500 domin kula da kanta da ’ya’yansu biyu.

Kotun da ke zamanta a kasar Birtaniya ta umarci Sarkin Dubai, wanda shi ne kuma Fira Ministan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), ya biya kudin ne domin bayar da kariya ga tsohuwar matar tasa da ’ya’yan daga abin da ta kira barazana da yake musu.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Moor, ya umarci sarkin da ya biya ta Fam miliyan 250 na kula da kanta nan take, kudi hannu, da karin Fam miliyan 290 da za a sa a banki domin biyan kudaden shekara-shekara na kuda da ’ya’yan.

Ya ce “Na gamsu cewa hakan na nufin duk da cewa Mai Martaba da ’ya’yan na bukatar kariya idan wani abu ya faru — duba da matsayinsu da kuma baraznaar ta’addanci da garkuwa da suke fuskanta — suna cikin hadari kuma suna bukatar tsauraran matakan tsaro a kasar nan.”

Kudaden da akalin kotun, Justice Moor ya ce a biya Gimbiya Haya da ’ya’yanta biyu su ne mafi yawa da kotu ta taba sawa a biya kan rabuwar aure a kasar Birtaniya.

Kotun ta ce akwai yiwuwar:

  • Sheikh Mohammed ya kitsa sace ’ya’yan nasa biyu, Gimbiya Latifa da Gimbiya Shamsa, gami da yin barazana ga mahaifiyarsu.
  • Ana kuma zargin shi da yin kutse a wayar tsohuwar matar tasa da wasu makusantanta biyar, ciki har da lauyoyinta, a yayin da ake ci gaba da shari’ar.
  • Jami’ansa sun yi yunkurin sayen wani rukunin gidaje a kan Fam miliyan 30m a kusa da gidan Gimbiya Haya da ke Berkshire wanda “barazana ce ga tsaronta”.

A lokacin da take Dubai akan ba Gimbiya Haya Fam miliyan 83 a shekara domin kula da gida da kuma Fam miliyan tara na kyaututtuka.

Amma a shari’ar ba ta nemi a biya da kudade ba, face dai tufafinta da gwala-gwalanta da ta rasa a sakamakon rabuwar aurensu.

Moor ya ce akwai yiuwar nan gaba ya sassauta kudaden kula da ’ya’yan idan suka zama baligai ko suka daidaita da mahaifinsu ko ya rasu, amma ba yanzu ba tukuna.

Wani mai magana da yawun Sheikh Mohammed ya ce: “Yana tabbatar da cewa a koyaushe iyalansa na samun kulawa. Kotu ta yanke hukuncinta kan kudaden kula da su, kuma ba ya sha’awar yin magana a kai.

“Yana rokon kafafen yada labarai da su mutunta hurumin ’ya’yan, su bar yi shisshigi game da abin da ya kebance su a kasar Birtaniya,” inji shi.