Wata kotu a Jihar Kano ta wanke Dagacin garin Saya-saya daga zargin aikata laifukan zamba, cuta, cin amana da kuma danne hakkokin masu unguwanninsa.
Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ce ta gurfanar da Dagacin, mai suna, Alhaji Tijjani Sarkin Fulani da kuma Muhammad Zubairu.
- Kotu ta daure barayin batirin mota da shekara 1
- An kasa gano dan wasan Ghana ba bayan girgizar kasar Turkiyya
Hukumar ta gurfanar da shi ne bayan zargin da wasu daga cikin ’ya’yan masu unguwannin da Allah Ya yi wa rasuwa suka yi, kan cin bashi da sunan iyayensu, tare da ci gaba da karbar albashinsu duk kuwa da cewa ba sa raye.
A zaman kotun na ranar Laraba, lauyan Gwamnantin Jihar Kano, Barista Zaharaddin Mustapha, ya gabatar wa kotun wata takarda daga ofishin Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano cewa bincike ya gano wadanda ake tuhumar ba su aikata laifukan da ake zargin su ba .
Bayan kammala gabatar da takaddar ce kotun ta wanke dagacin daga zargin tare da sallamar sa.
Dagacin garin saya-sayar Tijjani Sarkin Fulani ya bayyana farin cikinsa da yadda kotun ta wanke shi daga zargin.
An dai dauki tsawon lokaci ana gudanar shari’ar wacce ta dauki hankulan kungiyoyin kare hakkin dan Adam a Jihar Kano.