✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta wanke Janar din soja daga zargin satar biliyan N10.9

Kotun ta wanke Janar Jafaru Mohammed daga zargin badakalar Naira biliyan 10.9 na haram.

Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta wanke wani Janar din soja daga zargin satar Naira biliyan 10.9 da ya sa kotun ba da umarnin kwace wasu  kamfanoni da kadarori  28.

Kotun ta wanke Janar Jafaru Mohammed ne a yayin sauraron shari’ar da ake zargin wasu kamfanoni uku da safarar haramtattun kudade Naira biliyan 10.9 a gaban kotun.

A baya Aminiya ta kawo rahoto cewa a ranar 14 ga watan Fabrairu, Mai Shari’a  Nkeonye Maha ta ba da umarnin kwace wasu kadarori 28 da aka alakanta da wani babban hafsan soji.

Sai dai kuma takardar shari’ar da wakilinmu ya samu gani, Mai Shari’a Nkeonye Maha ta bayyana cewa Janar Jafaru ba shi da wata alaka da kamfanonin uku: kamfanin wurin taro na Marhaba Event Place Limited, kamfanin robobi na Aflac Plastics Limited, da kuma kamfanin mai na Atlasfield Integrated Limited.

A ranar 13 ga Mayu, 202o, Hukumar Yaki da Masu Ta’annati ga Tattalin Arziki (EFFC) ta shigar da kara tare da neman umarnin kotun na kwace kadarorin da take zargi an mallake su ne da kudaden haram.

Kafin kotun ta bayar da umarnin karshe na kwace kadarorin ga EFCC, kamfanonin uku ta hannun lauynasu, M. A. Belgore, sun kalubalanci kotun da cewa ba ta hurumin sauraron karar ake zargin Janar Jafaru Mohammed a ciki, saboda shi soja ne.

Lauyan kamfanonin ya bayyana cewa Sashe na 130(1) da kuma 170(1) (2) na Dokar Aikin Soja ta haramta wa irin kotun sauraron shari’ar da aka ambaci sunan Janar Jafaru a ciki, a matsayinsa na soja da ke kan aiki.

Amma alkalin ta yi watsi da hujjar, ta kuma amince da martanin lauyan EFCC, M A Belgore, cewa bukatar kwace kadara ba sai an kama mutum da laifi ba. Hasali ma kamfanonin uku ake kara a gaban kotun ba shi Janar Jafaru ba.

Ta ce, “Daga bayanan da ke gabana, mai shigar da kara (EFCC) sun shigar da bukatar kwace wasu kadarori a wurare daban-daban a Najeriya, mallakin wani Janar Aminu Kano (murabus) da mukarrabansa, da suka saya da kudaden da suka samu ta kazamar hanya.

“Na fahimci ba a ambaci sunan Janar Jafaru ba a cikin karar,” kamar yadda alkalin ta bayyana.