✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta wanke Shekarau daga zargin miliyan 950

Wata kotun daukaka kara da ke zamanta Kano ta wanke tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau daga zargin sama da fadi da Naira miliyan 950.…

Wata kotun daukaka kara da ke zamanta Kano ta wanke tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau daga zargin sama da fadi da Naira miliyan 950.

Hukumar EFCC ce ta gurafanar da shekarau bisa zargin sa da karbar kudin zabe a 2015 daga hannun tsohuwar Ministar Man Fetur Deizani Alison Madueke a zaben shugaban kasa.

Hukumar na zargin Shekarau da tsohon Ministan Harkokin Kasashen Waje, Ambasada Aminu Wali da Mansur Ahmad da karbar kudaden da aka raba wa wakilan jam’iyyar PDP a jihohi, inda ake zargin tsohon gwamnan da karbar naira miliyan 25.

Magoya bayan tsohon gwamnan a kafafen yada labarai na zamani na cike da murnar nasarar da suka samu na wanke jagoran nasu daga zargin da ake yi masa.