✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa Abduljabbar hukuncin Kisa ta hanyar rataya 

Lauyoyin Abduljabbar sun roki kotu ta yi masa sassauci

Kotun Musulunci da ke zamanta a Kano ta yanke wa Abduljabbar Nasir Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya kan laifin batanci ga Manzon Allah (SAW).

Da yake yanke hukuncin, alkalin Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a  Kofar Kudu, Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola, ya bayyana cewa ya yanke hukuncin ne bisa dogaro da sashe na 382 (b) na Shari’ar Jihar Kano ta shekarar 2000.

Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya ce kotun ta sami Abduljabbar da lafin yin kage da jafa’i ga Annabi Muhammad (SW) ta hanyar kirkirar kalmomin fyade da kwace da auren dole da mu’amalar biya wa macen da ba tasa ba bukatar da namiji wadanda malamin ya jingina su ga Manzon Allah (SWA).

Kafin yanke hukuncin sai da Mai sharia Ibrahim Sarki Yola ya yi waiwaye game da shari’ar, inda ya ce a takardar karar , Gwamnaatin Jihar Kano ta zargi malamin da yin kalaman batanci ga Annabi.

Alkalin ya bayyana cewa kalamarn batancin sun hada da, “mazinata da fyade da auren dole da yin aure ba sadaki” kalmomin da ya jingina ga Annabi (SAW) inda aka yada su a shafin Asshabul Kahfi na Facebook, kalmomin da wanda ake kara ya musanta su inda ya nuna cewa shi kore wadannan kalmomi yake yi daga janibin Manzon Allah (SAW) ba wai tabbatar da su ba.

Lokacin da kotun ta waiwayi bangaren lauyoyin wanda ake kara, sun nemi kotun ta yi masa sassuci, saboda a cewarsu, ya aikata laifin ne a bisa kuskure ga shi kuma shi magidanci ne da ke da iyali da kananan yara da suke bukatar kulawarsa.

Sai dai tun kafin sanar da hukuncin, fitaccen malamin ya nemi a gaggauta zartar masa da hukuncin kisa  bayan kotun Musuluncin ta sanar da kama shi da laifin yin batanci ga Manzon Allah (SAW).

A ranar Alhamis 15 ga watan Disamba 2022 Kotun Shari’ar Muslunci da ke zama a Kofar Kudu a birnin Kano ta tabbatar da laifin malamin, bayan wata 15 ana Shari’a a gabanta.

A yayin zaman kotun wadda Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ke jagoranta, Abduljabbar ya ce, “Ni ba na bukatar kai Ibrahim Sarki Yola ka yi min sassauci a wurin Allah kawai nake neman sassauci.

“Ina son a gaggauta zartar min da hukunci.

“Kuma ina amfani da wannan dama wajen ba masoyana hakuri kada su damu domin na san cewa zan yi mutuwa ta girma zan isa lahira a girmame.”

Tun a ranar 16 ga watan Yulin 2021 Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da Abduljabbar Kabara a gaban kotun bisa zargin sa da laifin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma tayar da hankalin jama’a, laifukan da suka saba da sashe na 385 da 375 na Kundin Shariar Pinal Kod.