✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa barawon doya 5 wata 6 a gidan yari

Ya ce a ranar ne da karfe 5:30 na yammaci, wanda ake zargi ya shiga wurin sana'ar Umar da ke kasuwar Galadima da ke Faggen…

’Yan sanda sun gurfanar da wani lebura mai shekaru 20 a gaban kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano, bisa zarginsa da satar doya guda biyar da ta kai ta N10,000.

A ranar Laraba ne dai aka gurafanar da matashin, mazaunin unguwar Rijiyar Lemo, bisa tuhumar sa da laifin sata.

Dan sanda mai gabatar da kara, Insfekta Abdullahi Wada, ya shaida wa kotun cewa mai kara Umar Nuhu mazaunin unguwar Birget ne ya shigar da kara ofishin ’yan sanda da ke unguwar Fagge a ranar 6 ga watan Satumba.

Ya ce a ranar ne da karfe 5:30 na yammaci, wanda ake zargi ya shiga wurin sana’ar Umar da ke kasuwar Galadima da ke Faggen ba tare da izini ba, ya kwashe masa doya.

Dan sandan ya ce sun kamo wanda ake zargin da doyar a hannu yana shirin sayar wa wani.

Laifin dai ya ce ya saba sashe na 133 na kundin shari`ar Musulinci.

Alkalin ya yanke wa wanda ake zargin hukuncin biyan tarar N6,000, ko kuma zaman gidan kaso na wata shida.