Kotu ta yanke wa Benzema hukuncin daurin talala na shekara daya | Aminiya

Kotu ta yanke wa Benzema hukuncin daurin talala na shekara daya

Karim Benzema
Karim Benzema
    Ishaq Isma’il Musa

Wata Kotu a Faransa ta yanke wa dan wasan kasar, Karim Benzema mai taka leda a Real Madrid, hukuncin daurin talala na shekara guda bayan samun hannunsa dumu-dumu a yunkurin bata sunan tsohon abokinsa a tawagar kasa, Mathieu Valbuena.

Kotun da ke zamanta a Versailles ta yanke wa dan wasan mai shekara 33 hukuncin ne bayan shari’ar da aka gudanar kan karar da ke tuhumar Benzema da yi wa Valbuena barazana ta hanyar amfani da wani hoton bidiyon batsa da ya nada shekaru 6 da suka gabata lokacin da suke taka leda a tawagar kasa.

Wannan takaddama a wancan lokaci ita ta zama dalilin da ya sanya ’yan wasan biyu wato Benzema da Valbuena mai shekaru 37 rasa gurabensu a tawagar kwallon kafar kasar gabanin dawo da Benzema a bana.

Bayanai sun ce Karim Benzema na cikin wasu mutum biyar da aka dawo da shari’arsu cikin watan jiya kan zargin yunkurin bata sunan Mathieu Valbuena tun a shekarar 2015.

Wadanda suka gabatar da kara a zaman kotun na ranar Laraba, sun ce Benzema ya yi amfani da kusancinsa ga Valbuena wajen matsa masa lamba don ganin ya biya masu yi masa barazana da bidiyon batsan kudin fansa duk da cewa yana da hannu wajen nadar bidiyon.

Baya ga daurin talala na shekara daya da Kotun ta Versailles ta yanke wa Benzema ta kuma umarci da ya biya tarar dala 84,000.

Wani rahoto da Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya wallafa ya ruwaito lauyan Benzema yana cewa zai daukaka kara.

Sai dai tun makonni uku da suka gabata ne Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa, Noel Le Graet, ya shaida cewa hukuncin da kotun za ta zartar ba zai yi tasiri a kan sana’ar dan wasan ba na tawagar Les Blues

Hakan dai ya nuna cewa dan wasan Real Madrid zai halarci Gasar Cin Kofin Duniya da za a buga badi a Qatar tare da Faransa bayan ya jagoranci tawagar kasar wajen lashe gasar Kofin Nahiyyar Turai na UEFA Nations League a watan Oktoba.