✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa dan Najeriya hukuncin rataya a Malaysia

Za dai a rataye mutumin ne bayan samunsa da laifi a tuhumar da ake masa.

Wata kotu a kasar Malaysia ta yanke wa wani dan Najeriya mai suna Alowonle Oluwajuwon Gilbert hukuncin kisa bayan samunsa da laifin kashe wata ma’aikaciyar jinya ’yar asalin kasar.

Za a kashe Alowonle ne ta hanyar rataya bayan an same shi da laifin kashe Siti Kharina, wacce uwa ce mai ’ya’ya uku.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Ab Karim Ab Rahman ya ce kotun ta yanke hukuncin ne bayan gamsuwa da hujjojin da aka gabatar a gabanta kan wanda ake zargin.

Siti Kharina dai ita ce babbar ma’aikaciyar jinya a asibitin Serdang na kasar, wacce aka neme ta  ta aka rasa tun ranar takwas ga watan Mayun 2019.

Rahotanni sun ce an yi mata gani na karshe ne a asibitin tun misalin karfe 4:00 na yammacin wannan ranar.

Daga bisani an tsinci gawarta ranar 15 ga watan Mayun 2015 da tabban yanka a wuyanta da kirjinta da kuma a kanta.

An dai tuhumi Alowonle ne da aikata laifin kisa, dogaro da sashe na 302 na kundin dokokin penal code na kasar.

Wanda ake zargin dai ya ce ya bar gidan matar ne ranar takwas ga watan Mayun 2019, shaidar da Mai Shari’ar ya karyata saboda ya ce ta saba da hotunan bidiyon da kyamarar sirri ta CCTV da ke gidan ta dauka ranar tara ga wata.

A cewar alkalin, wanda ake zargin ya gaza wanke kansa daga fallatsin jinin mamaciyar da aka samu a jikin rigar da ya sa ranar tara ga watan Mayu, wacce ke dauke da kwayoyin halittarta.