✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa mai facin mota hukuncin rataya saboda yin fashin N57,000

Matar da aka yi wa fashin ce ta gane mutumin

Wata kotun laifuka na musamman da ke Ikejan Jihar Legas a ranar Talata ta yanke wa wani mai faci hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda yi wa wata Nas fashin Naira 57,000.

Kotun, wacce ke karkashin Mai Shari’a Mojisola Dada, ce ta yanke hukuncin kan matashin mai suna Chidozie Onyinchiz, mai kimanin shekara 32.

Alkalin ta ce kotun ta tabbatar da laifuka ukun da ake zarginsa da aikatawa na hadin baki, fashi da makami da kuma shiga haramtacciyar kungiya.

Ta ce ko a baya wanda aka yanke wa hukuncin ya tabbatar wa ofishin ’yan sanda da ke Igando a Jihar Legas cewa shi da wacce aka yi wa fashin, Veronica Uwayzor, sun gane juna lokacin da aka kwace mata kudaden.

Mai Shari’a Mojisola ta ce, “Wacce aka yi wa fashin ta nuna wanda aka yanke wa hukuncin a matsayin daya daga cikin mutanen da suka yi amfani da almakashi suka kwace jakarta, wacce ke dauke da Naira 57,000 ta karfin tsiya, a tashar mota ta Akesan da ke Legas.

“Veronica ta kuma ce da wanda aka yanke wa hukuncin da wani abokin harkallar tasa mai suna Ediri Endurance, wanda yanzu haka ya cika wandonsa da iska, ba su rufe fuskarsu ba. Hakan ne ma ya sa ta iya gane su.

“Jimlar hujjojin da aka gabatar wa wannan kotun sun sa mun gamsu da cewa ya aikata laifukan da ake tuhumarsa da su.

“Saboda haka, wannan kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, Allah ya jikansa,” in ji Mai Shari’a Mojisola.

Tun da farko mai shigar da kara, Afolake Onayinka, ta shaida wa kotun cewa mutumin ya aikata laifin ne tare da wani wanda yanzu ya cika wandonsa da iska ranar 12 ga watan Agustan 2018.

Afolake ta ce laifukan sun saba da tanade-tanaden Kundin Manyan Laifuka na Jihar Legas na shekarar 2015. (NAN)