✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa mai walda hukuncin kisa ta hanyar rataya a Kogi

Alkalin ya yanke wa wanda ake tuhumar hukuncin kisa ta hanyar rataya, inda ya yi rokon Allah Ya jikansa.

Wata Babbar Kotu a Jihar Kogi ta yanke wa wani mai sana’ar walda mai suna Muritala Dare hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsa da laifin kashe wani abokin aikinsa mai suna Lukman Karim.

Kotun da ke zamanta a Lakwaja, babban birnin jihar, ta tabbatar da laifin kisan kai da Muritala ya aikata ta hanyar burma wa abokin sana’arsa fasasshiyar kwalba a wuya da hannu.

Da yake yanke hukuncin a ranar Alhamis, alkalin kotun mai sharia Josiah J. Majebi, ya tabbatar da laifin da Muritala ya aikata bayan kwararan hujjoji da dalilai da aka gabatar wa kotun kan laifin da ya aikata a ranar 16 ga watan Agustan bara.

Kotun ta ce laifin da Muritala ya aikata ya ci karo da sashe na 221 da ke cikin kundin dokokin final kot na Jihar Kogi.

Tun da farko dai jami’in dan sanda mai shigar da kara ya gabatar wa da kotun shaidu uku kari a kan hujjoji bakwai da suke tabbatar da laifin wanda ake tuhuma.

A kan haka ne mai shari’a Josiah ya ce kotun ta yanke wa wanda ake tuhumar hukuncin kisa ta hanyar rataya, inda ya yi rokon Allah Ya jikansa.