✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa matasa 3 hukuncin kisa ta hanyar rataya a Filato

Kotu ta yanke wa sau mutum uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun su da laifin kashe wani matashi

Kotu ta yanke wa sau mutum uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun su da laifin kashe wani mai suna Joseph Gosum.

Alkalin Babbar Kotun jihar da ke zamanta a garin Jos, Mai Shari’a Arum Ashom, ya yanke hukuncin ne zaman kotun na ranar Alhamis, inda ya ce kotun ta samu wadanda ake zargin da laifin hada baki da kuma aikata kisa.

Alkalin ya ce, “Terry Kefas da Samson James da Emmanuel Jah da kuma Patrick Nyam, a watan Disamban 2015 kun hada baki a yankin Gadabiu da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato domin kashe wani mai suna Joseph Gonsum ta hanyar daba mishi wuka a ciki.

“Wannan laifi ne a karkashin sashe na 97 da sashe na 221 na dokar ‘Penal Code’ da kuma dokar Arewacin Najeriya ta 1963.

“Kotu ta gamsu da hujjojin masu kara amma bangaren wadanda ake tuhuma ya kasa kawo wata kwakkwarar hujjar kare su.

“Kotu ta samu wadanda ake kara da laifi ta kuma yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya ko kuma allurar mutuwa.”

Lauyan masu kara, Barista Mantu Ishiaku, daga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Filato, ya ce hukuncin da aka yanke babbar nasara ce.

Ya kuma yaba bisa yadda kotun ta dauki lokacin wajen bin al’amarin cikin tsanaki tare da yanke hukunci daidai da doka.

Amma lauyan wadanda ake kara, Barista David Adudu ya bayyana rashin gamsuwa da hukuncin, da cewa “Zan yi nasarar hukuncin sannan in dauki matakin daukaka kara.”