✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa mutum 6 hukuncin kisa ta hanyar rataya a Osun

Kotuna ta sami mutanen ne da laifin kisa da kuma fashi

Wata Babbar Kotu a Jihar Osun a ranar Litinin ta yanke wa wasu mutum shida hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta same su da laifin kisan kai da fashi da makami.

Mutanen da aka yanke wa hukuncin sun hada da Hammed Rafiu da Rasidi Waidi da Kayode Sunday da Owolabi Bashiru da Mutiu Azeez da kuma Afolabi Mayowa.

Mai shigar da kara daga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar, Dele Akintayo, ya ce laifukan da suka aikata sun saba da tanade-tanaden sashe na 1(1) da na 2 (a) (b) na dokar hana fashi da makami da kuma shashe na R11 na kundin dokokin gwamnatin Najeriya.

Ya kuma ce Sunday da Owolabi da Rafiu da kuma Rasidi sun yi wa wani mai suna Victor Akinbile fashi ne ranar 26 ga watan Nuwamban 2018, dauke da muggan makamai.

Dele ya ce, “Sun bukaci Akinbile ya ba su Naira miliyan 10, amma sai ya tura musu miliyan uku ta banki, sannan suka karbi tsabar kudi a hannunsa da yawa, saboda sun yi barazanar kashe shi.

“Daga bisani kuma sun sace Akinbile inda suka saka shi a bayan wata mota kirar Toyota Camry, suka wuce da shi unguwar Dominion Camp da ke kan hanyar Ikirun zuwa Osogbo, inda suka banka wa motar wuta, lamarin da ya yi sanadiyyar konewarsa shi da motar kurmus,” in ji mai shigar da karar.

Dele ya kuma ce su kuwa Mayowa da Azeez, sun hada baki ne ranar daya ga watan Yulin 2018, inda suka yi wa wani dan acaba fashi, sannan daga bisani suka kashe shi.