Kotu ta yanke wa mutum biyu hukuncin rataya kan kisan kawunsu | Aminiya

Kotu ta yanke wa mutum biyu hukuncin rataya kan kisan kawunsu

Igiyar rataya
Igiyar rataya
    Ishaq Isma’il Musa da Iniabasi Umo, Uyo

Wata Babbar Kotu a Jihar Akwa Ibom ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifin kashe wani kawunsu mai suna Mista Imo Effiong Edet.

Kotun wacce mai shari’a Okon Okon ya jagoranci zamanta na ranar Laraba, ta yanke wa matasan biyu ’yan asalin Karamar Hukumar Ibesikpo Asutan hukuncin ne bayan ta tabbatar da zargin kashe kawunsu kan wani filinsa da suke son su mallake.

Mai sharia Okon ya ce kotun ta yanke wa matasan biyu hukuncin ne a karkashin tanadin da sashe na 326 ya yi a cikin mujalladi na biyu na kundin manya laifuka na dokokin Jihar Akwa Ibom.

Tun da farko dai ababen zargin biyu suka amsa laifin da ake tuhumarsu a gaban kotu, inda suka ce wani dan uwan kawunsu ne ya ba su kwangilar aikata wannan danyen aiki saboda ya yi kaka-gida wajen mallake gadon wata gona da mahaifinsu ya mutu ya bari.

Sun ce dan uwan kawun nasu ya yi musu alkawarin zai ba su wani kaso na gonar idan har sun samu nasarar kashe dan uwansa.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ababen zargin sun aikata wannan laifi ne tun a ranar 19 ga watan Nuwamban 2016, inda ake ci gaba da tsare su a gidan kaso gabanin kammala shari’ar a yanzu da ta kai ga an zartar musu da hukunci.

Bayanai sun ce daya daga cikin ababen zargin ya riga mu gidan gaskiya yayin da yake tsare a gidan gyara hali tun kafin a kammala shari’ar, lamarin da ya sanya kotun ta soke sunansa daga cikin takaddamar.

A bayanan da kotun ta gabatar yayin zartar musu da hukunci, ta ce bincike ya tabatar da cewa wadanda ake zargin sun kashe Mista Imo Effiong Edet ta hanyar sara da adda sannan suka yi masa yankan rago da wuka.

Da yake bayyana kisan a matsayin mafi kololuwar zalunci, mai shari’a Okon ya ce wadanda ake zargin sun aikata laifin ne da gangan.

A kan haka ne ya ce, kotun ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya, inda kuma ya yi addu’ar Ubangiji ya jikansu.