✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yanke wa tsohon Shugaban Tunisia daurin shekara 4 a gidan yari

An dai yanke masa hukuncin ne duk da yanzu yana Faransa.

Wata kotu a kasar Tunisia ta yanke wa tsohon Shugaban Kasar, Moncef Marzouki, hukuncin shekara hudu a gidan kaso saboda dukan wani jami’in tsaro, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito.

An dai yanke masa hukuncin ne duk da yanzu yana kasar Faransa, kuma a baya ya sha caccakar Shugaba Kais Saied tare da kiran jama’a su fito zanga-zanga.

Rahotanni sun ce an yanke masa hukuncin ne ranar Laraba, bayan an same shi da laifin yi wa tsaron kasar zagon kasa daga ketare da kuma kawo rudani a harkar diflomasiyyar kasar.

Sai dai a martaninsa ga hukuncin, Moncef, ya yi fatali da shi, inda ya ce, “Haramtaccen hukunci ne wanda haramtaccen Shugaban Kasan da ya yi wa Kundin Tsarin Mulki karan tsaye ya jagoranta.

Ya bayyana zarge-zargen da ake yi masa a matsayin bita-da-kulli, inda ya ce Shugaba mai ci ya kamata a yanke wa hukuncin.

Ya kuma sha alwashin ci gaba da yaki da abin da ya kira mulkin kama-karya har karshen rayuwarsa, ko da yake ya ce ba zai daukaka kara a kan hukuncin ba.

Sai dai lauyan tsohon Shugaban, Lamia Khemiri, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na  Faransa (AFP) cewa wanda yake karewar bai karbi karbi kowane irin sammaci ba, kuma bai san ainihin dalilin da ya aka gurfanar da shi ba.