✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yi watsi da bukatar Abduljabbar kan mukabala

Yana neman kotu ta soke rahoton alkalan mukabalarsa da malaman Kano.

Babbar Kotun Jihar Kano ta yi watsi da bukatar Sheikh Abduljabbar Kabara na jingine shawarwarin da ke kunshe cikin rahoton kwamitin alkalancin mukabalar da malaman Kano suka yi da shi.

A ranar 10 ga watan Yuli ne wasu malamai a Jihar Kano suka yi mukabala da Abduljabbar Kabara.

Mukabalar wadda aka gudanar bisa bukatar Abduljabbar Kabara a kan wasu mas’alolin da malaman suke zargin sa da yin batanci ga Manzon Allah (SAW) ya gudana karkashin jagorancin Farfesa Salisu Shehu.

Bayan kammala mukabalar, Farfesa Salisu Shehu ya ce malamin ya kasa amsa tambayoyin da aka yi masa, sai kauce-kauce yake yi, sannan ya shawarci Gwamnatin Jihar Kano da ta daukin matakin da ya dace a kan malamin.

Abduljabbar Kabara ya yi watsi da sakamakon mukabalar bisa hujjar cewa ba a yi masa adalci an saurare shi ba, sannan ba a ba shi isasshen lokaci ba.

Daga baya ya garzaya zuwa Babbar Kotun Jihar Kano, yana neman ta yi watsi da shawarwarin da ke cikin rahoton alkalan mukabalar.

Sai dai kuma Alkalin kotun kuma Babban Akkalin Jihar, Mai Shari’a Nura Sagir, ya yi watsi da bukatar malamin.