✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yi watsi da bukatar belin Abba Kyari

Kotu ta dage sauraron shari'ar Abba Kyari zuwa ranar 14 ga Maris, 2022.

Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da bukatar ba da belin shahararren dan sanda, Abba Kyari wanda ake zargi da safarar hodar Iblis.

Kotun ta yi watsi da bukatar ce a ranar Litinin, a yayin sauraron shari’ar da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miygun Kwayoyi (NDLEA) ta shigar tana zargin Abba Kyari da wasu hafsoshin ’yan sanda shida kan safarar kwayoyin.

Zaman kotun ya gudana ne kimanin mako guda bayan Gwamantin Tarayya ta amince ta mika Abba Kyari ga gwamnatin Amurka domin ya fuskanci wata shari’a a Amurka.

Abba Kyari na fuskantar zargin hannu a wata damfara da Dala miliyan 1.1 a Badakalar Hushpuppi, wanda ake zargin dan sandan da taimakawa wajen yin cutar da kuma tura kudaden da aka yi damfarar.

A lokacin zaman kotun da ke Abuja a ranar Litinin, ta ce nan gaba za ta duba bukatar da lauyoyin Abba Kyari suka gabatar mata na bayar da belinsa.

Da yake bayani bayan zaman kotun, lauyansa, ya bayyana cewa kotun za ta ci gaba da zaman sauraron sharia’ar a ranar 14 ga watan Maris da muke ciki.

Sai dai bai ce komai game da zaman kotun ba.