✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin batanci: Kotu ta hana Abduljabbar beli

Kotu ta sa a ci gaba da tsare malamin a kurkuku zuwa ranar 14 ga Oktoba, 2021.

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a birnin Kano ta ki amincewa da rokon da lauyoyin Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara suka yi a gabanta cewa ta bayar da belin sa.

Tunda farko dai Gwamnatin Jihar Kano ce ta yi karar Malam Abduljabbar Kabara a gaban kotun bisa zargin sa da laifin yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma tayar da hankalin jama’a.

A zaman kotun na ranr Alhamis, sabbin lauyoyin Malam Abduljabbar Kabara, karkashin jagorancin Barista Umar Muhammad sun roki kotun da ta bayar da belin malamin bisa hujjar cewa iyalan malamin suna cikin wani hali na wahala a dalilin rashinsa a kusa da su.

Lauyoyin sun kara bayyana wa kotun cewa idan malamin ya sami beli zai fi samin cikakken lokacin da zai yi bincike domin kare kansa a gaban kotu.

Sai dai lauyoyin gwamanti, wato masu gabatar da kara, karkashin jagorancin Barista Suraj Saida (SAN), sun kalubalanci bukatar belin da lauyoyin malamin suka shigar.

Lauyoyin gwamnatin sun kafa hujja da cewa abin da ake tuhumar Abduljabbar din da shi babban laifi ne wanda kuma ba a bayar da beli a kansa sai dai a kan wasu dalilai masu karfi.

Lauyoyin malamin sun nemi kotun da ta ba su kwafin shari’ar don sanin abin da ya gudana a dukkanin zaman da ta yi  a baya a kan shari’ar.

“Kasancewar yanzu muka shigo cikin shari’ar muna so kotu ta ba mu kwafin shari’ar don yin nazari game da zaman da ya gudana a kan shari’ar a baya,” Inji Barista Umar Muhammad.

Har ila yau lauyoyin na Abduljabbar Kabara sun nemi masu gabatar da kara da su zo da dukkanin shaidunsu a zaman kotun na gaba.

Lauyoyin gwamnatin sun amince da waxanann roko biyun na lauyoyin kariya inda suka ce ba su da suka akan hakan .

“Ba mu da suka a kan haka, mun amince a ba su kwafin shari’ar duba da cewa su sabbin lauyoyi ne da suka shigo shari’ar a yau; Mu kuma a shirye muke mu kawo shaidunmu ko da kuwa a yanzu ake nema,” inji Barista Saida Suraj.

Alkalin kotun Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya yi umarni da magatakardar kotun ya bayar da kwafin shari’ar ga lauyoyin malamin tare da umartar lauyoyin gwamnatin da su kawo shaidunsu a zama na gaba.

Mai Shari’a Sarki Yola ya bayyana kin amincewarsa game da neman belin Abduljabbar inda ya kafa hujja da cewa laifin da ake tuhumar malamin da shi babban laifi ne wanda ba a bayar da beli a kansa sai dai a kan wasu kebantattun hujjoji wadanda kuma a cewar alkalin hujjojin da lauyoyin malamin suka bayar suna da rauni kuma ba su cikin hujjojin da za a iya bayar da beli akansu, don haka ya bayar da umarnin ci gaba da tsare wanda ake zargi a gidan gyaran hali.

Daga nan kotun ta dage sauraren shari’ar zuwa ranar 14 ga watan Oktoba, 2021.