✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yi watsi da karar da aka shigar da Tinubu kan amfani da takardun bogi

Kotu ta ce karar da Jam'iyyar AA ta shigar kan Tinubu shisshige ne da kuma tsoma baki cikin matsalar cikin gidan wata jam'iyya.

A ranar Talata Babbar Kotun Tarayya  da ke Abuja ta yi watsi da karar da jam’iyyar AA ta shigar kan dan takarar Shugaban Kasa na APC,  Bola Tinubu, kan cewa ya yi amfani da takardun bogi.

Da yake watsi da karar, Alkalin Kotun, Mai Shari’a Obiora Egwuatu, ya ce karar da Jam’iyyar AA ta shigar dakatacciya ce sakamakon ta cika wa’adin kwana 14 da doka ta ayyana ba tare da an saurare ta ba, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki na 1999 ya tanadar.

Ya kara da cewa, wannan ya sa karar ta rasa hurumin kotun ta saurare ta balle kuma ta amsa bukatun mai karar.

Kazalika, Alkalin ya ce mai karar ta yi shisshigi kasancewar ta tsoma bakinta cikin matsalar cikin gida da ta shafi wata jam’iyya daban.

Haka nan, rashin mutunta tsarin kotu na daga cikin dalilan da suka sanya Alkalin yin watsi da karar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewar, baya ga Tinubu, karar mai lamba FHC/ABJ/CS/954/2022 da Jam’iyyar AA ta shigar din, ta shafi har da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da Jam’iyyar APC.

Jam’iyyar AA ta yi zargin takardun shaida na bogi Tinubu ya gabatar wa INEC wadanda ke nuna ya halarci Sakandaren Gwamnati da ke Ibadan da kuma Jami’ar Chicago.

(NAN)