✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta yi watsi da karar neman hana Atiku tsayawa takara

Wata kungiya tana zargin cewa ba a Najeriya aka haifi Atiku ba.

Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yi watsi da karar da ke kalubalantar cancantar takarar tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya Atiku Abubakar.

BBC ya ruwaito cewa, wata kungiya mai da’awar kare hakkin dan Adam ce ta shigar tana neman kotun ta hana Atiku tsayawa takara bisa kafa hujjoji na cewa ba dan kasar nan ba ne.

Kungiyar mai suna Egalitarian Mission for Africa ce ta shigar da karar tana kalubalantar cewa ba a Najeriya aka haifi Atiku ba, don haka ta ke neman kotu ta hana shi tsayawa takarar shugaban kasa.

Sai dai alkalin kotun Mai Shari’a Inyang Ekwo ya yi watsi da karar yana mai cewa ba hurumin kungiyar ba ne, kamar yadda Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito.

Watsi da karar na zuwa bayan gwamnantin Jihar Adamawa ta shaida wa Kotun cewa Atiku cikakken dan jihar ne wanda aka zaba gwamna a 1999, kuma ya zama Mataimakin Shugaban Kasa daga 1999 zuwa 2007.