✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta yi watsi da karar zaben Yahaya Bello

Kotu ta tabbatar da zaben Yahaya Bello

Kotun Daukaka Karar Zaben Gwamnan Jihar Kogi ta yi watsi da karar da ke kalubalantar zaben Gwamna Yahaya Bello a zaben da ya kawo shi wa’adin mulkinsa na biyu.

Alkalan kotun karkashin Mai Shari’a Adamu Jauro sun yi watsi da karar da dan takarar jam’iyyar PDP a zaben, Musa Wada ya shigar, bisa hujjar kasa tabbatar da zarginsa na cewa an yi magudi a zaben.

Sun kuma yi watsi da karar neman soke zaben da ‘yar takarar jam’iyyar SDP Natasha Akpoti ta shigar bisa zargin saba ka’idoji, da kuma wadanda ‘yan takarar jam’iyyun DPP da APP suka shigar na zargin an cire sunayensu a zaben.

Gabanin yanke hukuncin kotun na ranar Asabar, lauyoyin Musa Wada, Jirin Okutepa (SAN) da Solomon Umoh (SAN) sun bayyana wa kotun cewa wanda suke karewa ya cika sharuddan da suka kamata a sanar da cewa shi ne zaben gwamnan jihar Kogi.

Sun kuma kafa hujja da hukuncin kotun sauraran kararrakin zabe gamnan jihar na ranar 23 ga watan Mayu, wanda ya ce zaben na cike da aringizon kuri’u da kuma bambanci tsakanin adadin kuri’un da aka jefa da yawan masu zaben kananan hukumomin Kabba, Ajaokuta, Lokoja, Okehi, da kuma Olamaboro.

Sai dai Alex Izinyon (SAN) da Ahmed Raji (SAN) da kuma Joseph Daudu (SAN), wadanda su ne lauyoyin hukumar zabe ta INEC da jam’iyyar APC da Gwamna Bello, a martaninsu, sun bukaci kotun ta yi watsi da karar saboda masu shigar da ita sun kasa kawo gamsasshiyar hujjar tabbatar da zargin da suke yi na magudi ko aringizon kuri’u a zaben na ranar 16 ga watan Nuwamban 2019.

Zuwa yanzu dai Musa Wada ya lashi takobin daukaka kara zuwa Kotun Koli.