✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Birtaniya ta sami Ike Ekweramadu da laifin safarar sassan jikin dan Adam

An same shi ne da laifin lokacin da ya kai 'yarsa

Wata kotun kasar Birtaniya ta sami tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Ike Ekweramadu da matarsa, Beatrice, da laifin safarar sassan jikin dan Adam.

A cewar jaridar Guardian ta Birtaniya, kotun ta sami ma’auratan ne tare da ’yarsu, Sonia da kuma wani likita, Obinna Obeta, da laifin.

An same su ne da hannu dumu-dumu a kan kai wani matashi kasar ta Birtaniya da nufin yin amfani da kodarsa bayan shafe mako shida ana yi masa gwaji a Old Bailey.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Jeremy Johnson, zai yanke masa hukunci nan gaba kadan, in ji jaridar.

Yanke hukuncin na ranar Alhamis shi ne irinsa na farko tun lokacin da dokar hana bautar da dan Adam ta zamani ta fara aiki.

A bara ne dai aka kama Ekweramadu da matar tasa a Birtaniya da nufin yankar kodarsa don a dasa wa Sonia.

Bayanai sun nuna cewa an yi karyar shigar da shi kasar a matsayin dan uwan Sonia a kan kudi £80,000 a asibitin Royal Free Hospital da ke birinin Landan.

Mai shigar da kara a kotun, Hugh Davies KC, ya ce iyalan da kuma likitan sun hada baki wajen hada-hadar wacce ta saba wa dokokin kasar.