✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Daukaka Kara Ta Bada Umarnin Ci gaba da Tsare Nnamdi Kanu

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin dakatar da aiwatara da hukuncin da ta yanke na sakin shugaban Harmatacciyar Kungiyar…

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin dakatar da aiwatara da hukuncin da ta yanke na sakin shugaban Harmatacciyar Kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Gwamnatin Tarayya, ta yi ikirarin cewa sallamar Kanu aka yi ba a wanke shi ba, inda ta garzaya kotu domin bukatar ta dakatar da aiwatar da hukuncin.

Kotun ta dakatar da aiwatar da hukuncinta na baya, kan kamo Kanu daga Kenya zuwa Najeriya tare da ajiye tuhumar da ake masa na ta’addanci.

Alkalan Kotun uku bisa jagorancin Haruna Tsamani sun ce zai fi dacewa a jira hukuncin karar da ke gaban Kotun Koli tukuna.

Ta kuma bayar da umarnin mika kundin hukuncin da ta yi a baya ga kotun koli, nan da kwanaki bakwai.

Gwamnatin Tarayya dai ta daukaka kara a gaban Kotun Koli, tana bukatar ta janye hukuncin kotun daukaka kara, wanda ya yi watsi da sauran tuhume-tuhume da take yi wa Kanu.

Gwamnatin Tarayyar ta bakin lauyanta, David Kaswe, ta sanar da Kotun Daukaka Kara cewa Kanu ya nuna za a iya nemansa a rasa muddin ba ya tsare, la’akari da yadda ya yi makamancin haka a shekarar 2017.

Sai dai lauyansa, Mike Ozekhome (SAN), ya bukaci kotun ta yi watsi da ikirarin gwamnatin, kasancewar wanda yake karewa gudun tsira da rai ya yi a 2017, bayan da sojoji suka kai masa farmaki har gidansa da ke  Umuahia da ke Jihar Abia, har mutane 28 suka rasa ransu sanadiyyar hakan.

Lauyan ya kuma ce ci gaba da tsare Kanu har ya wuce ranar da aka yanke masa, tauye masa hakkinsa ne, yayin da a cewarsa sakin sa kuma zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya a kasar.