✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun daukaka kara ta tabbatar da takarar Bwacha a Taraba

Kotun ta tabbatar da shi a matsayin dan takarar Gwamnan Taraba a Jam’iyyar APC

Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar gwamnan Jihar Taraba na jam’iyyar APC.

Da suke yanke hukunci a zaman da aka yi a Yola, a ranar Alhamis, kwamitin alkalai uku karkashin jagorancin Mai Shari’a Tani Yusuf Hassan, ta bayyana Bwacha a matsayin wanda ya dace ya tsaya takara a Jam’iyyar APC.

Kotun ta bayar da umarnin mika sunansa ga Hukumar Zabe ta Kasa  (INEC) a matsayin dan takarar Jam’iyyar APC a zaben 2023.

A baya wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke zaben Bwacha a matsayin dan takarar gwamna, inda ta kalubalanci zaben da aka gudanar na fid-da-gwani a watan Mayu, 2022.

Kotun da ke sauraren karar ta saurari karar da ake yi na soke zaben Bwacha bisa hujjar cewa zaben bai bi dokar zabe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima ba.