✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da zaben Ademola Adeleke

Ta umarci jam’iyyar APC da dan takararta su biya tarar N500,000.

Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta tabbatar da zaben Ademola Adeleke a matsayin gwamnan Jihar Osun.

A wannan Juma’ar ce wani kwamitin alkalai mai mutane uku karkashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Lawal Shuaibu ya bayyana cewa, dan takarar jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar, Gboyega Oyetola ya gaza tabbatar da zargin magudi da aringizon kuri’u a zaben da ake yi wa jam’iyyar PDP.

A hukuncin da aka yanke, Kotun Daukaka Karar ta kuma bai wa jam’iyyar APC da dan takararta umarnin biyan tarar kudi N500,000.

Aminiya ta ruwaito cewa, a yau aka yanke cewa Kotun Daukaka Kara, za ta yanke hukunci kan karar da gwamnan Jihar Osun Ademola Adeleke ya shigar gabanta, inda yake kalubalantar soke zaben da ya ba shi nasara da Kotun Sauraron Korafe-Korafen Zabe ta yi a baya.

Adeleke da jam’iyyarsa ta PDP sun bukaci Kotun Daukaka Karan da ta jingine hukuncin kotun baya da ta soke nasararsa.

A ranar 27 ga watan Janairu ne, Mai Shari’a Tetsea Kume, na Kotun Sauraron Korafe-Korafen Zabe a lokacin yanke hukunci, ya ce Hukumar Zabe ta INEC ba ta bi tanade-tanaden Dokar Zabe da na Kundin Tsarin Mulki yadda ya kamata ba.

A cewar kotun, idan aka cire kuri’un da ake zargin an yi aringizo, Adegboyega Oyetola na APC ya samu yawan kuri’u 314,921 yayin da Ademola Adeleke na PDP ya samu kuri’u 290,266.