✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta daure Sunday Igboho a Jamhuriyar Benin

Sai dai kotun ta ki amincewa da bukatar tisa keyarsa zuwa Najeriya.

Kotun Daukaka Kara da ke birnin Kwatano na Jamhuriyar Benin ta ba da umarnin daure mai fafutukar kafa kasar Yarabawan nan, wato Sunday Igboho a gidan yari.

Sai dai kotun ta ki amincewa da bukatar tisa keyarsa zuwa Najeriya, yayin da zai ci gaba da zama a can har zuwa lokacin da za su kammala bincike.

Kotun, wacce ya kamata ta fara sauraron karar tun kusan karfe 10:00 na safiyar Litinin ta hana ’yan jarida da magoya bayan Igbohon shiga cikinta lokacin da ta fara zama da misalin karfe 5:00 na yamma.

Aminiya ta gano cewa daga bisani an tarwatsa magoya bayan nasa wadanda suka yi cincirindo a wajen kotun, suna tsoron za a iya tisa keyarshi zuwa Najeriya.

Gwamnatin Najeriya dai na zargin Igboho me da safarar makamai, tayar da zaune tsaye da kuma yunkurin ballewa.

Ta kuma bukaci a tiso mata keyarshi zuwa gida.

An dai kama Igboho tare da matarsa Ropo a Filin Jirgin Saman Kasa da Kasa na Cardinal Bernardin a makon da ya gabata lokacin da suke kokarin sulalewa zuwa Jamus.

Amma a ranar Alhamis, kotun ta sallami matar, wacce ’yar asalin kasar Jamus ce yayin da shi kuma ta ba da umarnin tsare shi a kurkuku.

A ranar daya ga watan Yuli ne dai Hukumar Tsaro ta DSS ta ayyana Igboho a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bayan jami’anta sun yi dirar mikiya a gidansa da ke Ibadan, suka kashe biyu daga cikin yaransa sannan suka kama 12.

Sabon Salon Karbar Kudin Fansa: Dabara ko Wauta?