✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Kano ta tsare ’yan fashi 5 a gidan yari

Sun kutsa cikin kamfanin ’yan kasar China inda suka yi fashi da makami

Kotu ta daure wasu mutum biyar a gidan kurkuku kan zargin fashi da makami a Jihar Kano.

An gurfanar da mutane masu shekaru 20 zuwa 48 ne a wata Kotun Majistare a Kano bisa zargin hadin baki da aikata fashi da makami da mallakar makami ta haramtacciyar hanya.

Jami’ar dan sanda mai shigar da kara, Asma’u Ado ta shaida wa kotun cewa mutanen sun aikata laifin ne a ranar 13 ga Janairu, 2021 a kauyen Zainawa na Karamar Hukumar Gezawa ta Jihar.

Ta bayyana cewa an kama su da misalin karfe 12:30 na dare bayan sun hada baki da gugun abokanan huldarsu sun yi wa wasu ’an Chanisawa biyu fashi .

Asma’u ta ce mutanen da ake tuhumar sun kutsa cikin kamfanin da ake samar da maganin sauro na ‘Wexiang Mosquito Company’ da ke kauyen Zainawa inda suka yi wa wani mai suna Ananthachai Amnalbandit da matarsa fashin wayoyinsu na salulu guda hudu.

Ta ce mutanen sun yi amfani da bindigogi da adduna da sanduna a yayin fashin sannan sun yi awon gaba da kwamfuta da agogon hannu biyu da kimarsu ta kai N137,000.

Sai da mutanen da ake tuhumar sun musanta aikata laifin.

Alkaline kotun, Mai shari’a Mustapha Sa’ad-Datti, ya bayar da umarnin dakatar da sauraren karar har sai an ji shawarar da Babban Darakta mai tuhuma na jihar.

Ya kuma dage sauraron shari’ar zuwa ranar 7 ga watan Afirilun 2021.