✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli ta rantsar sabbin Manyan Lauyoyin Najeriya 72

Babban Alkalin Najeriya bai halarci taron rantsar Manyan Lauyoyin ba

Kotun Koli ta Najeriya ta rantsar da sabbin Manyan Lauyoyin Najeriya (SAN) guda 72 a safiyar Litinin.

Sai dai Shugaban Alkalan Najeriya, Mai Shari’a Muhammad Tanko, wanda shi ya kamata ya jagoranci taron bai halarta ba.

Sakamakon haka alkali mafi girma a Kotun Koli, Mai Shari’aOlabode Bodes-Rhodes Vivour ce ta rantsar da sabbin Manyan Lauyoyin a madadinsa.

An ba wa lauyoyin matsayin na SAN ne a matsayin shaidar gwanancewa a manazarta kuma masu kare hakki.

A watan Nuwamba ne Kwamitin Alfarmar Ayyukan Sharia ya amince da daga martabar lauyoyi 72 zuwa matsayin SAN.

Da take ba su rantsuwa, Mai Sharia Rhosdes-Vivour ta yi jan kunne ga masu saba wa umarnin kotu.

Sabbin Lauyoyin Najeriya kan karbi rantsuwar fara aiki ne a bikin farkon Shekarar Shari’a ta Kotun Kotu.

Bisa al’adar taron an shekara-shekara, Shugaban Alkalan Najeriya ne ke jagorantarsa; ba a samu bayanin dalilin rashin halartar Mai Shari’a Muhammad Tanko taron na 2020 ba.