✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli ta soke dokar haramta sanya hijabi a makarantun Jihar Legas

Alkalan sun ce hana dalibai Musulmi sanya hijabi tauye musu ’yancinsu na yin addini da tsare mutuncinsu da kuma walwalarsu ne

Kotun Koli ta soke dokar da ta haramta wa dalibai Musulmi sanya hijabi a makarantu a Jihar Legas.

Kwamitin Alkalai shida na Kotun Kolin ne ya yanke hukuncin a zaman kotun na ranar Juma’a, ya kuma bayyana cewa umarnin ya takaita ne a makarantun gwamnatin jihar.

Alkalan sun bayyana haramta wa dalibai Musulmi ’yancinsu na sanya hijabi a matsayin tauye hakkinsu na yin addini da tsare mutuncinsu a matsayinsu na ’yan Adam da kuma walwalarsu, sabanin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

Wannan hukunci dai ya sanya farin ciki da murna a zukatan al’ummar Musulmi, inda Shugaban Kungiyar Dalibai Musulmi ta Najeriya (MSSN) Reshen Jihar Legas, Miftahudeen Thanni tare da mambobin kungiyar suka yi ta kabbara tare da hamdala.

Alkalan da suka yanke hukuncin su ne Mai Shari’a Olukayode Ariwoola da Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun da Mai Shari’a John Inyang Okoro da Mai Shari’a Uwani Aji da Mai Shari’a Mohammed Garba da Mai Shari’a Tijjani Abubakar da kuma Mai Shari’a Emmanuel Agim.

Hukuncin Kotun Kolin ya tabbatar da makamancinsa, wanda Kotun Daukaka Kara ta yanke da farko, inda ta soke hana dalibai Musulmi sanya hijabi a makarantun jihar.

A hukuncin da ta yanke da farko, kotun daukaka karar ta bayyana cewa hana dalibai Musulmi sanya hijabi ba komai ba ne face nuna musu wariya.