✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Kolin Indiya ta share hanya ga mabiya addinin Hindu su gina wajen bauta a filin Masallacin Ayodhya

Kotun Kolin kasar Indiya a karshen mako ta yanke hukuncin mika wani fili da ake takaddama a kansa ga mabiya addinin Hindu, wanda hakan ke…

Kotun Kolin kasar Indiya a karshen mako ta yanke hukuncin mika wani fili da ake takaddama a kansa ga mabiya addinin Hindu, wanda hakan ke nufin an share musu hanyar kafa wajen bauta a masallacin Ayodhya da ke Arewacin India, inda wani gungun mabiya addinin Hindu suka rushe masallacin da aka gina tun karni na 16  a shekara 25 da suka gabata.

Da suke yanke hukunci alkalan kotun su biyar sun yi ittifaki game da daya daga cikin dadaddun rigingimun da aka fi tayar da jijiyar wuya a kansa, inda suka ce ya kamata a bai wa Musulmin yankin wani fili na daban domin gina masallaci.

Shari’ar wadda ta shafe fiye da shekara 20 ana yi game da  filin mai girman murabba’in eka 2.77 an faro ta ce tun 1992, yayin da rusa masallacin ya haifar da mummunar zanga-zangar da ta yi sanadin salwanatar rayuka 2,000.

A yanzu za a mika filin ne ga wata gidauniya – wadda gwamnati za ta kafa da za ta sa ido wajen gina wurin ibadar mabiya addinin Hindu.

Shugabannin addinan Hindu da na Musulunci sun yi ta nanata kira ga mabiya da lallai a kai zuciya nesa tare da zaman lafiya – bayan wannan hukunci.

Mabiya addinin Hindu sun yi imanin cewa a wannan fili da ake takaddama kansa ne aka haifi ubangijinsu mai suna Rama da suke bautawa yayin da Musulmi suka gina masallacinsu a wajen ibadar na ’yan addin Hindu.

Zafaryab Jilani, shi ne lauyan da ya tsaya wa al’ummar Musulmin da suka shigar da karar, ya ce ba su gamsu da hukuncin ba; sai dai sun yi kiran a kwantar da hankali.  “Yanzu an bayar da filin masallacin ga wani bangare. Wannan babu adalci da daidaito a ciki, sam-sam,” inji shi.

’Yan sanda da sojoji na sintiri

An tsaurara tsaro a duk fadin kasar, musamman a yankin na Ayodhya, wanda ’yan sanda fiye da 5,000 da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro ke sintiri – yayin da aka haramta duk wani jerin gwanon jama’a.

Firayi Ministan Indiya Narendra Modi, wanda ya yi kiran kai zuciya nesa, ya wallafa a shafinsa na Tiwita cewa bai kamata a kalli hukuncin a zaman na wani ya yi nasara ko wani ya fadi ba.

“Ina kiran Indiyawa kowa ya fi bai wa hukuncin kallon wani abu da zai dada karfafa al’adar nan ta zaman lumana, hadin kai tare da yi wa Indiya kyakkyawar fata,” kamar dai yadda ya wallafa.

“Hakan ya gwada cewa za a iya warware duk wani batu da ake takaddama kansa cikin ruwan sanyi ta hanyar shari’a. Ya kuma sake tabbatar da ’yanci da kamanta adalci na sashen shari’ar kasarmu. A fili yake, hukuncin ya gwada yadda kowa yake daidai da kowa a idon shari’a.”

Ana yi wa hukuncin kallon nasara ce ga jam’iyyarsa ta ’yan kishin kasa ’yan Hindu ta Bharatiya Janata Party. Batun wajen ibadar ya taka muhimmiyar rawa wajen kara wa jam’iyyar tagomashi a idon Indiyawa. A yayin yakin neman zaben bana, batun ya taimaka  wajen dawo da jam’iyyar kan madafun iko, inda ta yi alwashin sake gina wajen bautar.

An gabatar da batun a gaban Kotun Kolin Kasar a shekarar 2010 bayan da masu jayayya daga addinan biyu – Musulmi daHindu – suka kalubalanci wani hukuncin da ya tanadi mika kashi biyu cikin uku na filin a mabiya addinin Hindu domin gina wajen ibadarsu, yayin da daya kason kuma Musulmin ne za su gina masallaci, a ainihin filin  da masallacin da aka rusan yake.

Zaman lafiya fiye da komai

Zaman tankiya da zullumi ya samu gindin zama a yankin Ayodhya, inda da dama mazauna yankin suke dokin ganin an gine wurin ibadar, sai dai Musulmi da mabiya addinin Hindu sun ce sun zaku su ga karshen wannan shari’a da ta shafe tsawon lokaci ana tafkawa.

“Muna son ganin an warware batun gaba daya,” inji Arun Kumar, wani mabiyin addinin Hindu.

“Muna da cikakkiyar amannar cewa za a gina wurin ibadar, sai dai zaman lafiya shi ne kan gaba da komai,” inji shi.

An kai karar Asaduddin Owaisi

An kai karar wani jagoran Musulmi Asaduddin Owaisi ga ’yan sanda game da furucin da ya yi kan hukuncin da kotun ta yi a karshen mako. Wani lauya ne a yankin Bhopal ya zargi Owaisi da kalaman tunzuri da nuna kyama.  Bayan hukuncin an jiyo Owaisi na cewa al’ummar Musulmi ba sa bukatar kyautar fili mai girman eka biyar.

Lauyan mai suna, Pawan Kumar, ya gabatar da kara kan Owaisi a caji ofis na ’yan sandan Jahangirabad game da kalaman da ya yi kan hukuncin na Ayodhya ranar Asabar. An shigar da karar ce bisa zargin ya yi kalaman tunzura jama’a.

Jim kadan bayan hukuncin da Kotun Kolin ta yanke, inda ta bayar da umarnin a samar wa al’ummar Musulmin wani fili mai girman eka biyar – Owaisi ya ce tayin a bai wa Musulmin wannan filin abin a yi watsi da shi ne, kuma ba za su yi maraba da shi ba.

“Musulmi matalauta ne, amma za mu iya hada taro da sisi domin sayen fili mai girman eka biyar domin gina masallaci. Ba ma maraba da tayin kyautarku,” kamar yadda aka ruwaito Owaisi na fada – wanda hakan ya janyo masa suka a ranar 9 ga watan Nuwamba.