✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Kolin Kenya ta tabbatar da nasarar Ruto a zaben Shugaban Kasa

Hukuncin ya share fagen rantsar da sabon Shugaban

Kotun Kolin Kasar Kenya, ta tabbatar da nasarar da tsohon Mataimakin Shugaban Kasar, William Ruto ya samu a zaben Shugaban Kasar.

Matakin dai ya biyo bayan yanke hukuncinta kan wasu kararraki da babban abokin hamayyarsa, Raila Odinga ya shigar.

Shugabar kotun mai mutane bakwai, Martha Koome ce ta yanke hukuncin bai-daya a ranar Litinin.

“Mun ayyana zaben zababben Shugaban Kasa a matsayin ingantacce kuma halastacce,” inji ta.

A ranar 15 ga watan Agusta ce Shugaban Hukumar Zabe ta Kasar, Wafula Chebukati ya ayyana Ruto a matsayin wanda ya lashe zaben da kaso 50.4 cikin 100 na kuri’un, yayin da Raila Odinga kuma ya sami kaso 48.8.

A wani gagarumin rarrabuwar kai daf da bayyana sakamakon zaben, hudu daga cikin Kwamishinonin zaben bakwai sun yi watsi da shi.

Amma Koome, ta ce “ban da sukar da suka yi na sa’o’i 11 na tsarin tantancewar. Kwamishinonin hudu ba su nuna wata shaida da ke nuna cewa an yi magudi a zaben ba”.

Ta kuma ce, kotun ba ta samu wata shaida da ke nuna cewa, an tafka magudin zabe, ta hanyar kutse ta na’urar intanet a hukumar zaben ba, kamar yadda bangaren Odinga ya yi zargi.

Hukuncin Kotun Kolin dai a yanzu ya share fagen rantsar da Ruto mai shekara 55 a matsayin Shugaban Kasar Kenya na biyar a cikin kwanaki masu zuwa.