✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotun MDD ta kama Ratko Mladic da yi wa Musulmi kisan kiyashi

An tabbatar da daurin rai-da-rai ga tsohon shugaban sojin Bosnia kan hallaka Musulmi

Kotun Daukaka Kara ta Majalisar Dinkin Duniya tabbatar da laifin tsohon shugaban sojin Sabiyawan Bosnia, Ratko Mladic, na yi wa Musulmi kisan kare dangi a yakin Bosnia tsakanin shekarun 1992 zuwa 1995.

Alkalan kotun ta musamman kan manyan laifuka ta Majalisar Dinkin Duniya sun kuma tabbatar da hukuncin daurin rai-da-rai da aka yanke wa mista Mladic kan laifin.

Hukuncin da alkalan biyar na kotun da ke birnin Hague suka yanke a ranar Talata shi ne na karshe, daga kansa babu maganar daukaka kara.

Shekara 26 bayan kisan kiyashin da aka yi a Srebrenica, hukuncin ya kawo karshen shari’ar mutum na karshe dan kasar Bosnia da ake masa shari’ar kisan kare dangi a kotun.

Alkalin da ta jagoranci zaman, Prisca Matimba Nyambe, daga Zambia ta ce kotun ta yi watsi da daukaka karar da Mladic ya yi ‘dungurumdum dinta’.

Kotun ta kuma yi watsi da daukaka karar da masu shigar da kara suka gabatar na neman wanke shi daga wata tuhumar kisan kare dangin da ke da nasaba da shafe kabila a farkon soma yakin.

Yanzu dai Mladic ya bi sahun tsohon ubangidansa a siyasa, kuma tsohon Shugaban Kasar Sabiyawan Bosnia, Radovan Karadzic, wajen zaman kason rai-da-rai saboda hannu a kitsa zubar da jinin da aka yi a yakin na Bosnia inda fiye da mutum 100,000 suka mutu, wasu miliyoyi kuma suka rasa muhallansu.

A baya, Mladic ya kasance wani gawurtaccen soja mai fankama wanda ake wa lakabi da “Mahaucin Bosnia”.

Mladic shi ne ya jagoranci dakarun sojin da suka aikata miyagun ayyuka da suka hada da ‘shafe kabila’ da mamaye Sarajevo da ma rura wutar yakin a lokacin da yake ganiyarsa a 1995 a kisan kiyashin Srebrenica.

Kisan kiyashin da aka yi wa Musulmi fiye da dubu takwas, ciki har da mata da yara kanana, a Srebrenica, shi ne kadai kisan kiyashin da aka taba aikatawa a duk nahiyar Turai tun bayan Yakin Duniya na II.

Matan da aka kashe mazajensu sun kasance a wajen kotun a yayin da ake yanke hukuncin.

Babbar Jami’ar MDD kan kare hakkin dan Adam,  Michelle Bachelet, ta yi na’am da hukuncin.