✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Musulunci ta daure barawon talo-talo wata 2 a Kano

An yanke wa matashin hukuncin daurin wata biyu a gidan gyaran hali da tarar kudi N20,000.

Wata kotun shari’ar Musulunci a Kano ta yanke wa wani matashi mai shekara 23 daurin wata biyu a gidan gyaran hali saboda satar talo-talo.

Da yake yanke hukuncin, Alkalin kotun, Malam Mansur Ibrahim, ya ce an yanke wa matashin, dan unguwar Rimin Kebe da ke Kano hukuncin ne bayan ya amsa laifin da ake tuhumar shi da aikatawa.

Kazalika, alkalin ya yanka wa matashin tarar kudi N20,000 sannan ya ba shi umarnin biyan diyyar N16,000 ga mai talo-talon.

Tun da farko mai shigar da kara, Abdullahi Muhammad, ya shaida wa kotun cewa matashin ya aikata laifin ne a unguwar Rimin Kebe a ranar 1 ga watan Janairu.

Ya ce matashin ya tsallaka gidan wani mutum sannan ya yi masa awon gaba da talo-talo, ya kuma je ya sayar a kan kudi N7,000.

Muhammad ya ce laifin ya saba da sashe na 133 na kundin laifuka na shari’ar Muslunci na Jihar Kano.