✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Myanmar ta daure Aung San Suu Kyi shekara 4 a kurkuku

Kotun ta sameta ne da laifin tayar da zaune tsaye da kuma karya dokokin COVID-19.

Wata kotun kasar Myanmar ta yanke wa hambararriyar jagorar kasar, Aung San Suu Kyi, hukuncin daurin shekara hudu a gidan gyaran hali.

Kakakin Rundunar Sojin kasar, Zaw Min Tun, ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) cewa an yanke mata hukuncin ne ranar Litinin, bayan kotu ta sameta da laifin tayar da zaune tsaye da kuma karya dokokin cutar COVID-19.

Zaw Min ta ce Misis Aung San ta samu hukuncin daurin shekara biyu a kan kowanne daya daga cikin laifukan guda biyu.

Kazalika, kotun ta kuma daure tsohon Shugaban Kasar, Win Myint, na tsawon shekara hudu bisa makamantan laifukan, ko da yake ta ce ba za a yi garajen kai su gidan kukuku ba tukunna.

“Za su fuskanci wasu tuhumce-tuhumcen daga wuraren da suke tsare yanzu a babban birnin kasar na Naypyidaw,” inji Zaw Min.

Shari’ar dai wacce aka gudanar a birnin Naypyidaw an gudanar da ita ne a cikin sirri ba tare da ba kafafen yada labarai damar kallonta ba, yayin da sojoji suka kuma hana lauyan Aung San Suu kyi daga yin hira da ’yan jarida da sauran jama’a.

Hukuncin na ranar Litinin dai shi ne irinsa na farko cikin jerin tuhumce-tuhumcen da ake yi wa tsohuwar Shugabar mai kimanin shekara 76, tun bayan hambarar da gwamnatinta ta farar hula a watan Fabrairun bana.