✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ku bar Adamawa ko ku fuskanci hukuncin kisa —Fintiri ga ’yan bindiga

Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri ya gargadi masu ayyukan ta’addanci da satar mutane su bar Jihar Adamawa ko su fuskanci hukuncin kisa. A ziyararsa ga Gangwari…

Gwamnan Adamawa, Ahmadu Fintiri ya gargadi masu ayyukan taaddanci da satar mutane su bar Jihar Adamawa ko su fuskanci hukuncin kisa.

A ziyararsa ga Gangwari Ganye, Alhaji Umaru Sanda ziyara a Karamar Hukumar Ganye, Fintiri ya ce gwamnatin jihar ba za ta saurara wa kowa ba ko wata kungiya mai alaka da garkuwa da mutane ko ayyukan ta’addanci a jihar.

“Bari na sake maimaitawa, na sake fito da komai fili, idan ka san wani mai satar mutane ko mai alaka da su, to ko dai ya bar Jihar Adamawa lami lafiya ko kuma idan mun kama shi ya fuskanci hukuncin kisa.

“Cin kashin ya isa haka, ba za mu lamunci irin wadannan ayyukan taaddancin a jiharmu ba da mutanen cikinta ke kaunar zaman lafiya.

“Gwamnatin Jiha tare da hadin guiwar hukumomin tsaro za su yi aiki tare da saraukuna da shugabannin aluma wajen fatattakar yan taadda daga jiharmu,” inji shi

Ya ci gaba da cewa, duk wanda yaki jin wannan gargadin to ba shakka ba ya mai kaunar zaman lafiyar jamaa ba ne don haka shi ma ba zai zauna lafiya ba.