✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ku dauki makamai ku kare kanku daga ’yan bindiga – Gwamnan Bauchi

Bala ya ce ba zai yiwu a bari a ci gaba da aikata ta'addanci ba.

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi kira ga al’ummar yankin Karamar Hukumar Alkaleri da su dauki makamai don kare kansu daga ’yan ta’adda.

Bala ya yi wannan kira ne ranar Alhamis a lokacin da ya ziyarci fadar Sarkin Yelwan Duguri, Alhaji Adamu Mohammed Duguri, yayin ziyarar da kai kauyukan Rimi da Gwana da Yalwan Duguri.

Ya ziyarci kauyukan ne domin jajanta musu kan harin da ’yan bindiga suka kai musu a baya-bayan nan.

Gwamnan ya ce, ba za a bari ta’addancin ya ci gaba da aukuwa ba, dole a dauki matakin dakatar da shi ta kowane hali.

A cewarsa, “Na bai wa rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro umarnin su kula duk wani dan bindiga da aka kama saboda ba zai yiwu mu ci gaba da asarar mutanenmu haka kawai ba.

“Mun rasa mutum 12 a nan, an kona gidaje, wasunsu ma da ransu aka kona su.

“Dole yanzu ku zama mazaje, kada ku bari wadannan bata-garin su cutar da ku, ku mike ku dauki makamai ku kare kanku da kasarku,” in ji Bala.

Idan za a iya tunawa Aminiya ta rawaito ’yan bindiga suka kashe mutum 17 a harin da suka kai kauyen Rimi da ke jihar.