✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ku fara dibar masu yi wa kasa hidima a ayyukan kwangilolinku – Minista ga kamfanonin gine-gine

Minista a Ma’aikar Ayyuka da Gidaje, Umar Ibrahim EL-Yakub, ya bukaci kamfanonin gine-gine na Najeriya su fara dibar matasa masu yi wa kasa hidima da…

Minista a Ma’aikar Ayyuka da Gidaje, Umar Ibrahim EL-Yakub, ya bukaci kamfanonin gine-gine na Najeriya su fara dibar matasa masu yi wa kasa hidima da wadanda ba su jima da kammala karatu ba yayin aiwatar da ayyukan kwangilolinsu.

Ya ce yin hakan zai taimaka wa matasan matuka su sami karin gogewa kan yadda ake yin ayyukan a zahiri, kamar yadda aka koyar da su a makarantunsu.

Ministan ya bayyana haka ne ranar Juma’a, lokacin da yake duba sashe na daya na aikin titin Kano zuwa Maiduguri, wanda ya tashi daga Kano ya wuce ta Wudil ya tsaya a Shuarin, a Jihar Jigawa.

Sai dai Umar EL-Yakub ya koka kan yadda ya ce sassa biyu na aikin wanda yake da tsawon kilomita 560, wanda aka bayar da kwangilarsa tun a 2006, na tafiyar hawainiya.

Ya ce, “Wannan aiki ne da ya shafe kusan shekara 15 zuwa 16 da gwamnatocin baya suka yi watsi da shi, kafin zuwan gwamnatin Shugaba Buhari.

“Ba mu jima da kammala taron masu ruwa da tsaki kan ayyuka ba na Najeriya na bana wanda aka yi wa taken zamanin kammala ayyuka. Don haka, muna so a kammala wannan aikin ko dai a cikin wata uku na karshen wannan shekarar, ko kuma a farkon badi.

“Tuni aka kammala sashe biyu daga cikin sassa biyar na wannan hanyar. Ragowar guda biyun; Kano zuwa Shuarin da kuma Damaturu zuwa Maiduguri, su ma ya kamata a kammala su nan ba da jimawa ba,” inji shi.

Ya kuma ce an saka aikin titin a tsarin samar da kudade na Bankin Musulunci wato SUKUK, domin tabbatar da aikin bai sami tangardar biyan kudi ba.

Tun da farko dai, Manajan Aikin titin, Injiniya Roy Hungushi, ya shaida wa Ministan cewa an kammala gina dukkan gadojin sama guda biyu, da na rafuka guda uku da ke kan sashen hanyar, kuma yanzu haka kimanin kaso 70 cikin 100 na hanyar an kammala ta kuma ana amfani da ita.

Sai dai ya roki Ministan ya tabbatar ana sakar musu kudaden kwangilar a kan lokaci domin su sami damar kammalawa nan da lokacin da aka dibar musu.